21 Oktoba 2024 - 06:38
Isra’ila Ta Kai Hari Bam A Lebanon Kusa Da Filin Jirgin Saman Beirut

A daren jiya ne dai gwamnatin yahudawan sahyoniya ta sake kai wani kazamin harin bam a yankunan kudancin birnin Beirut. Wadannan hare-haren sun kai har tashar jirgin saman Beirut.

 Jiragen yakin gwamnatin yahudawan sahyoniya sun kai hare-hare a yankunan kudancin birnin Beirut, Darreh Bakaa da ke gabashi da kudancin kasar Lebanon.

Sannan Jiragen saman gwamnatin sahyoniyawan sun yi ruwan bama-bamai a gine-gine a garuruwan Baalbek da Hermel da kuma garuruwan Ali Nahari da Bednayl da ke yankin Bekaa a gabashin kasar Labanon.

 A kudancin kasar dai an kai harin Nabatie da garuruwan Ma’arakah, Kufra da Yatar.

 Har ila yau an kai harin ne a reshen Mu’assasa Al-Qardul-Hasana da ke kusa da filin jirgin saman Rafiq Hariri a kudancin birnin Beirut. Kakakin gwamnatin yahudawan sahyoniya ya yi ikirarin cewa wannan kungiya ita ce mai samar da kudi ga kungiyar Hizbullah a kasar Labanon.

 Kamfanin dillancin labaran kasar Lebnon ya habarta cewa, sakamakon harin da ‘yan mamaya suka kai kan wata motar daukar marasa lafiya a kan hanyar “Be’iril-Salsal” a garin Kharba Salem da ke gabashin birnin Tire kudancin kasar Lebanon ya bar asara mai yawa.